August 31, 2023

TINUBU YA WARE NAIRA BILIYAN 50 DON SAKE GINA YANKUNAN AREWA.

 

A wani labari da kafar yaɗa labarai ta BBC Hausa ta wallafa a shafinta na yanar gizo ta bayyana cewa; shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ware naira biliyan 50 don aikin sake gina yankunan arewa. Mataimakin shugaban ƙasar Sanata Kashim Shettima shine ya sanar da haka a lokacin da majalisar ƙoli kan harkokin addini a ƙarƙashin mai alfarma Sarkin Musulmi Alh. Sa’adu Abubakar III ta kai ziyara fadar shugaban kasa a yau alhamis.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ci gaba cewa “shugaban ƙasar ya ware naira biliyan 50 don aikin sake gina yankuna arewa maso yamma da arewa maso gabashin ƙasar. Sanata Kashim Shettima ya ce matakin wani yunƙuri ne na magance matsalar tsaro da yankunan ke fama da ita.

Tun da farko shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya ce “sauye-sauyen tattalin arziki da ke haifar da matsin rayuwa da gwamnatinsu ke yi, sakamakon cire tallafin man fetur za su amfani ‘yan ƙasar da dama a nan gaba. Tinubu ya ce yana da yaƙinin sauye-sauyen za su amfani ‘yan ƙasar a nan gaba musamman a fannonin Ilimi da ayyukan yi da lafiya da abubuwan more rayuwa.

“Najeriya ta ɗauki alƙawari, kuma sauye-sauyen za su kawo mana ci gaba mai ɗorewa, za mu gina ƙasarmu, ta yadda ‘ya’yanmu za su yi alfahari da ita”, in ji shugaban ƙasar.

Shugaban ya shaida wa majaliar ƙolin cewa gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da gwamnatocin jihohi domin bunƙasa harkokin noma da kiwon dabbobi, domin fara fitarwa zuwa ƙasashen ƙetare, lamarin da zai samar da ayyukan yi tare da samar da kudin shiga ga ƙasar.

 

©Bbc Hausa.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “TINUBU YA WARE NAIRA BILIYAN 50 DON SAKE GINA YANKUNAN AREWA.”