
Jami’ai a Gabon sun dakatar da gidajen yada labarai na gwamnatin Faransa na wani dan lokaci da suka hada da TV5 Monde da France 24 da Radio France International (RFI).
Hakan ta faru ne saboda jami’ai na ganin tashoshin ba su nuna adalci da daidaito a lokacin babban zaben da ya gudana a ranar Asabar ba.
Gidan rediyon Faransa ya bayyana damuwarsa kan matsaloli bayan zaben, musamman saboda rashin intanet da kuma sanya dokar hana fita.
Wani mai magana da yawun gwamnati, Rodrigue Mboumba Bissawou, ya ce an rufe intanet da kuma sanya dokar hana fita ne saboda hana ƴaduwar tashin hankali bayan zaben.
A ranar Lahadin da ta gabata, kamfanin da ya mallaki gidajen talabijin din da aka dakatar, France Médias Monde ya ce “ya yi na dama kuma da mamakin wannan dakatarwar ta wucin-gadi wanda hakan zai hana mutanen Gabon amintattun labarai da bayanai.”
Dama dai kasashe irinsu Burkina faso, Mali da kuma Jamhuriyar Nijar inda sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula sun dakatar da kafafen yada labaren na faransa musamman Rfi da kuma France 24.
©voh