November 10, 2021

​Saudiyya Na Amfani Da Kungiyar Kasashen Larabawa Domin Muzguna Wa Lebanon

Daga shafin Hausatv


A ranar wannan Litinin 8 ga watan Nuwamba mataimakin babban sakataren kungiyar kasashen larabawa Husam Zaki ya kai ziyara kasar Lebanon, inda ya gana da manyan jami’an gwamnatin kasar da suka hada da shugaba Micheil Aoun da kuma firayi minista Najib Mikati.
Ziyarar dai tana da alaka ne da takaddamar da Saudiyya ta tayar tsakaninta da gwamnatin kasar ta Lebanon, dangane da batun furucin George Kardahi, ministan yada labarai na kasar, inda ya ce yakin da Saudiyya take kaddamarwa kan al’ummar kasar Lebanon shekaru 7 a jere wauta ce, kuma dole ne a kawo karshen hakan.

Husam Zaki ya bukaci gwamnatin Lebanon da ta yi wa Kardahi murabus daga kan mukaminsa, sannan kuma ta aiwatar da wasu bukatu na gwamnatin Saudiyya, matukar tana bukatar Saudiyya ta sake dawo da alaka a tsakaninsu.

Wannan matakin dai yana zuwa ne bayan da George Kardahi ya tsaya kan bakansa, na cewa abin da ya furta mahangarsa ce ba mahangar gwamnatin Lebanon ba, kuma ya fadi hakan ne kafin ya zama minista, saboda haka lamari ne wanda ba shi da alaka da abin da gwamnatin Saudiyya ke kokarin alakanta shi da shi.

Saudiyya dai ta bayyana cewa kungiyar Hizbullah ita ce babbar matsala a wurinta a Lebanon, a kan haka ta bukaci gwamnatin Lebabnon da ta kwace makaman Hizbullah da kuma daikile tasirinta a cikin Lebanon, amma ministan harkokin wajen Lebaon ya sheda cewa lallai Saudiyya ta bukaci abin da ba zai taba yiwuwa ba.

SHARE:
Labaran Duniya, Rahotanni 0 Replies to “​Saudiyya Na Amfani Da Kungiyar Kasashen Larabawa Domin Muzguna Wa Lebanon”