November 23, 2021

​Bankin IMF Ya Shawarci Najeriya Da Ta Cire Tallafin Mai Da Na Wutar Lantarki

Daga shafin Hausatv


Bankin IMF ya shawarci Najeriya cewa yawan kuɗaɗen da ta ke kashewa idan auna su da waɗanda ta ke samu, to za’a ci gaba da samu wawakeken giɓi a kowace shekara, kamar irin wanda aka samu a bana cikin 2021.

Bayanin IMF ya ce idan aka cire tallafin fetur da na kuɗin lantarki, an kama hanyar daidaita matsalolin ƙaranci kuɗi a hannun gwamnati kenan.

Sa dai kuma a cewar bayanin, “Amma kuma tilas sai ita gwamnatin ta bijiro wasu tsare-tsaren da za ta rage wa talakawa tsadar rayuwa, sakamakon matsin da za su shiga idan an ƙara kuɗin fetur da kuɗin wutar lantarki.

IMF ta ƙara da cewa, tafiyar-hawainiyar da sabon tsarin canjin kuɗaɗe ke yi, tare da rashin tabbas na kasa maido maƙudan kuɗaɗen da ɓarayin gwamnati suka sace suka ɓoye a waje, ya rage ƙarfin yawan shigowar hannayen jari masu nauyi a Najeriya.”

Wasu ƙarin matsalolin da tattalin arzikin Najeriya ke ci gaba da fuskanta, a cewar IMF, sun haɗa da ƙarancin kayan da Najeriya ke fitarwa waje.

A kan haka sai IMF ta nemi Najeriya ta fito da wani tsari da zai hana raguwar kuɗaɗen ajiyar Najeriya da ke waje.

Bayanin ya ce, ya kamata Najeriya ta aiwatar da wanan tsari na kara kudin man fetur da wuta lantarki daga nan zuwa farko shekara ta 2022, saboda yawabn bashin da ke kanta.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Bankin IMF Ya Shawarci Najeriya Da Ta Cire Tallafin Mai Da Na Wutar Lantarki”