October 9, 2021

​Afghanistan: Daesh Ta Dauki Alhakin Harin Ta’addanci A Kan Masallacin Juma’a A Kunduz

Daga Jaridar Hausatv


​Afghanistan: Daesh Ta Dauki Alhakin Harin Ta’addanci A Kan Masallacin Juma’a A Kunduz
Kungiyar ‘yan ta’addan daesh ta dauki alhakin harin ta’addancin da aka kai jiya a kan masallata a lokacin sallar Juma’a a cikin gundumar Kunduz a kasar Afghanistan.

Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, an kai harin ta’addanci ne a jiya a kan wani masallacin Juma’a a Lardin Kunduz na kasar Afghanistan, a lokacin da ake sallar Juma’a, kuma mutane da dama suka rasa rayukansu da kuma jikkata.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, wani dan ta’adda ne da ya yi jigidar bama-bamai ya tarwatsa kansa a tsakiyar masallata a lokacin sallar Juma’a a masallacin mabiya mazhabar Ahlul bait a yankin Khan Abad da ke cikin gudumar Kunduz.

Mai magana da yawun kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya fitar da bayani da ke cewa, wasu ‘yan ta’adda sun kai wa ‘yan uwanmu musulmi hari a lokacin sallar Juma’a, kuma wasu da dama sun yi shahada wasu kuma sun jikkata.

Ya zuwa yanzu dai akalla mutane ne aka tabbatar da rasuwarsu yayin da kuma wasu fiye da 200 suka samu munanan raunuka.

Bayan kai harin babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma daga bisani kungiyar ‘yan ta’addan Daesh ta fitar da sanarwa da ke cewa, ita ce take da hannu a wannan harin.

Tun kafin hakan dai an yi zargin cewa kungiyar ce ta kai wannan hari, wadda a baya ma ta kai wasu makamantansu a kan wuraren ibada da makarantu a cikin kasar ta Afghanistan, tun kafin da kuma bayan kwace iko da kasar Afghanistan da Taliban ta yi, kungiyar ta Taliban dai ta sha alwashin shiga.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Afghanistan: Daesh Ta Dauki Alhakin Harin Ta’addanci A Kan Masallacin Juma’a A Kunduz”