October 24, 2023

Ɗalibin Jami’a Ya ‘Kashe’ Ɗan Sakandare A Bauchi

Ana zargin dalibin aji biyar a Jami’ar ABU da luwadi da kuma kashe wani dan sakandare a garin Misau da ke Jihar Bauchi

Wani dalibin aji biyar a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU) ya shiga hannu kan zargin luwadi da kuma kisan wani dan sakandare mai shekaru 17 a Jihar Bauchi.

Dalibin jami’ar wanda ke karatun a fannin likitancin dabbobi ya fada komar Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) ne bayan an tsinci gawar dan sakandaren a yashe a gefen titin wajen gari a Karamar Hukumar Misali ta Jihar Bauchi.

Kwamandan NSCDC na jihar, Ilelaboye Oyejide, ya ce bayan tsintar gawar a yashe cikin farin kyalle, “aka kai ta Babban Asibitin Misau, likitoci suka tabbatar rai ya yi halinsa, aka mika ta ga iyayensa suka yi masa jana’iza.”

Ya ce daga bisani hukumar ta kaddamar da zuzzurfan binciken da ya kai ga kama dalibin jami’ar, wanda aka gano tattaunawarsu ta waya da marigayin.

“A tattaunawarsu da mamacin ta waya da muka gani, wanda ake zargin ya yi wa marigayin tayin luwadi ta hanyar tura masa hoton tsiraicinsa.

“Da marigayin ya je wurinsa ne wanda ake zargin ya soka masa wuka a ciki, ya nade gawar a cikin farin kyalle ya jefar a gefen titi, inda aka tsince ta.”

Kwamandan na NSCDC ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin a yayin da ake masa tambayoyi, kuma a bisa hakan za a gurfanar da shi a kotu.

Oyejide ya bayyana cewa wanda ake zargin ya shaida wa masu bincike cewa dan sakandaren ne zaro wuka ya yiwo kansa da ita, suka yi ta kokawa, inda a garin kare kansa ya soka wa marigayin wukar ta yi ajalinsa.

Wanda ake zargin ya ce, “Na tsorata sosai saboda ban taba fuskantar irin haka ba a rayuwata. Shi ya sa na nade shi a kayan na jefar da gawar a gefen hanyar bayan gari.”

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Ɗalibin Jami’a Ya ‘Kashe’ Ɗan Sakandare A Bauchi”