October 31, 2023

ƳAN’UWANA MATASA KU MATSO KU JI, LALLAI KU MU KULA DA WANNAN!

Daga Malam Bakir Ibrahim 

Daga Abu Basir Cewa: “Na Shiga wajen Ummu Humaidah (Matar Imamus Sadiƙ, Mahaifiyar Imamul Kazim A)) don in yi mata ta’aziyyar wafatin Mijinta Imam Sadiƙ (A), sai ta ɓarke da kuka nima sai kama kuka saboda yadda take kukan”. Bayan ta ɗan natsa ta sarara, sai ta kalli Abu Basir ta ce da shi “Da a ce kana nan a wajen Abi Abdullahi (As-Sadiƙu (A) a lokacin cikawarsa, da ka ga abin mamaki”

Abu Basir sai ya tambaye ta “Me ya faru?” Ta amsa masa da cewa: “Buɗe idonsa ya yi, sannan ya ce: Ku tattaro min duk wani wanda yake da kusanci da ni. Ba mu bar kowa ba sai da muka tattaro su duka” Ba kuma wanda a cikin su ya san ko mene ne dalilin yin wannan kiran a wannan lokacin kuma me za a yi?

Bayan sun tattaro duk makusantan nashi kamar yadda Imam ɗin (A) ya umarta, sai ya kalle su kallo irin na bankwana tare da barin wasiyya irin na wanda yake dab da wucewa zuwa ga Allah. Sai Imam (A) ya ce musu: “Lallai cetonmu -a ranar Alƙiyama- ba za ta sami me yin sako-sako (wulaƙanta/wasa da) salla ba”
{Al-Amaliy -Saduƙ: 572}

_______________________
D A R A S I !

Dubi fa! Imami ma’asumi ne wanda muke fatan in an je lahira a cikin inuwarsu kaɗai za mu iya fakewa. Amma kalli yadda ya shimfiɗa mana wata ƙa’ida wacce ita za ta iya ba mu damar samun shiga alfarmarsu ɗin nan, ƙa’idar kuwa ita ce: DOLE NE MU KULA DA LAMARIN BAUTAR ALLAH. Bugu da ƙari a bisa ɗabi’ar ɗan’Adam, duk abinda aka faɗa masa ana kan gargara to wannan ɗin yakan ƙara fito masa da girma da muhimmancin wannan abin ne, shi ya sanya Imam (A) ya nusashe he mu a daidai lahazarsa ta ƙarahe.

Yanzu wannan bai isa ƙara tsoro da firgici a zuciyata ba? Tabbas ya isa!
Don haka: Ya zama wajibi ga duk mai fatan samun ceton waɗan nan jiragen na tsira, to ya massala kiyaye wannan ƙa’idar iya iyawarsa. Na ambato matasa ne saboda mafi yawa mu ne muka fi bayyana da irin wannan dabi’a ta yin sako-sako da ramarin bautar Ubangiji. Ku mu yunƙura don gyara, Allah kuma ya gyara mana!

SHARE:
Makala 0 Replies to “ƳAN’UWANA MATASA KU MATSO KU JI, LALLAI KU MU KULA DA WANNAN!”