August 24, 2021

Ƴan sanda a Kano sun cafke kwararren mai kwacen waya

Daga Baba Abdulƙadir
Hukumar ƴan sanda ta  jihar Kano ta ce, jami’anta sun cafke wani matashi da ya jima yana ƙwace wa mutane wayoyin hannu.
Hakan na cikin wata sanarwa da Jam’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sanda na jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai yau Litinin.
Ya ce, an kama matashin Adamu Sadi da aka fi sani da da Daddy a unguwar Rijiyar Lemo a yau.
DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ƙara da cewa tun da fari wani mutum ne ya shigar da ƙorafin cewa matashin ya yanke shi da wuƙa tare da ƙwace masa waya tun a ranar 9 ga wannan wata da muke ciki na Agusta.
Inda ya ce, bayan ƴan sanda sun baza komar neman sa ne cikin ikon Allah da kwazon jami’anmu gashi sun yi nasarar cafke shi.
SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Ƴan sanda a Kano sun cafke kwararren mai kwacen waya”