August 13, 2021

Ƴan Bindiga Sun Saki Kwamishinan Yaɗa Labarai Na Jihar Neja

Daga Baba Abdulƙadir
Rahotanni daga daga jihar Neja sun tabbatar da cewa ƴan bindiga, sun sako kwamishinan yada labarai na jihar Neja, Alhaji Muhammed Sani Idris da suka yi garkuwa da shi.
Jaridar Ahlulbaiti
ta ruwaito cewa, ɓata garin sun saki Kwamishinan ne da misalin karfe 9:30 na daren jiya Alhamis a wani wuri da ke cikin garin Suleja.
Haka kuma rahotonni sun bayyana cewa, tuni aka mika shi asibiti domin duba lafiyarsa.
Kazalika, wasu majiyoyi sun ce ba a biya kudin fansa ba kafin a saki kwamishinan.
Da yake magana bayan sakin nasa, kwamishinan ya gode wa Allah da ya kare shi a lokacin da ya ke hannun ‘yan bindigar inda ya shafe kwanai hudu a can.
Indai ba’a manta ba, a  daren Lahadin da ta gabata ne dai yan bindiga suka kutsa kai Kauyen Tunga dake karamar hukumar Tunga ta jihar Neja, da misalin karfe 1:00 na daren wayewar Litinin inda suka yi awon gaba da kwamishi nan.
SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Ƴan Bindiga Sun Saki Kwamishinan Yaɗa Labarai Na Jihar Neja”