August 10, 2021

Ƴan bindiga sun sace kwamishina a jihar Neja

Daga Baba Abdulƙadir
Wasu gungun ƴan bindiga sun yi garkuwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar Neja Malam Muhammad Idris. Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Ahmed Matane ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.
Rahotanni sun tabbatar da cewa sakataren gwamnatin ya ce, ƴan bindigar sun je gidan kwamishinan ne wanda ke ƙauyen Baban Tunga da ke yankin ƙaramar hukumar Tafa da misalin ƙarfe 1:00 na daren jiya Lahadi inda suka yi awon gaba da shi.
Haka kuma ya ce, ɓata garin sun isa gidan ne akan a kallah babura 15 ɗauke da manyan bindigogi da muggan makamai.
Shi ma a nasa ɓangaren jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Wasi’u Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin.
Hazalika ya ce, rundunar za ta yi cikakken ƙarin bayani ga manema labarai nan ba da jimawa ba.
SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Ƴan bindiga sun sace kwamishina a jihar Neja”