March 18, 2023
Ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa NUJ, reshen jihar Kano, tayi tofin ala tsine kan harin da wasu ƴan dabar siyasa suka kaiwa wakilin Premier Radio Ashiru Umar. Harin, wanda yayi sanadin raunata Ashiru, tare da farfasa wayar sa, ya faru ne a lokacin da yake tsaka da aikin ɗaukar bayanan zaɓe. Shugaban ƙungiyar, Mallam Abbas Ibrahim ya bukaci yan sanda su tsananta bincike a kan lamarin, domin kamo ɓatagarin tare da ladabtar da su.
